Home Labaru Majalisa Za Ta Kama Shugaban Hukumar Kula Da Farashin Mai In Ya...

Majalisa Za Ta Kama Shugaban Hukumar Kula Da Farashin Mai In Ya Ki Bayyana

314
0
Majalisa Za Ta Kama Shugaban Hukumar Kula Da Farashin Mai In Ya Ki Bayyana
Majalisa Za Ta Kama Shugaban Hukumar Kula Da Farashin Mai In Ya Ki Bayyana

Majalisar wakilai ta yi barazanar kama babban sakataren hukumar kula da farashin albarkatun man fetur Abdulkadir Seidu, matukar ya ki amsa gayyatar kwamitin kudi na majalisar a karo na uku.

Kwamitin dai ya bukaci ganin shugaban hukumar ne bisa rashin biyan kudaden shiga da hukumar ba ta yi ba daga shekara ta 2014 zuwa 2019.

Haka kuma, kwamitin na bincike hukumomi da ma’aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya da ba su biyan kudaden shiga cikin asusun gwamnatin tarayya.

Shugaban kwamitin James Falake ya yi barazanar a lokacin yayin zaman kwamitin na ranar Talatar da ta gabata a Abuja, bayan ya kori jami’an hukumar da suka zo domin wakiltar shugaban hukumar Abdulkadir Seidu.

Kwamitin majalisar dai, na bukatar Seidu ya gabatar da kansa a gaban kwamitin a ranar 30 ga watan Maris.

Haka kuma, shugaban kwamitin binciken asusun ajiyar hukumomi da ma’aikatu Wole Oke ya gayyaci manajan darakta na hukumar kula da tashohin jiragen ruwa Habib Abdullahi da direktan Kudi na hukumar su bayyana a gaban kwamitin cikin kwanaki bakwai kan rashin yin binciken kwakwaf a asusun hukumar na tsawon shekaru hudu.