Home Labaru Kiwon Lafiya Annobar Corana: Gwamnati Ba Za Ta Kara Daukar Aiki Ba-Ministar Kudi

Annobar Corana: Gwamnati Ba Za Ta Kara Daukar Aiki Ba-Ministar Kudi

383
0
Mutum 4 ke nan suka kamu da cutar a fadin jihar Kano, kawo yanzu
Mutum 4 ke nan suka kamu da cutar a fadin jihar Kano, kawo yanzu

Gwamnatin tarayya ta dakatar da daukar aiki a daukacin ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Ministar kudi Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa kasa jim kadan bayan kamala taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Shamsuna Ahmed ta kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan ma’aikata albashi, kuma ba za ta sallami ma’aikata ba, amma ba za a sake daukar sabbin ma’aikata ba.

Zainab ta kuma bayyana wasu matakai da gwamnati ta dauka domin dakile yaduwar cutar Corona kan tattalin arzikin kasa.

Daga cikin matakan akwai rage farashin man fetur da gyara kasafin kudin 2020 da kara yawan danyen man da aka hakowa zuwa ganga miliyan 2 da budu dari 18 a rana da kuma sauya kudin harajin hukumar kwastam da ayyukan walwala da jin kai da dai sauran su.