Tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu, ya musanta zargin da hukumar EFCC ta yi ma shi cewa ya yi rub-da-ciki a kan naira biliyan 7 da miliyan 65 yayin da ya ke kan gadon mulki.
Yayin tabbatar da gaskiyar sa, Uzor Kalu ya ce jihar Abia ba ta taba samun irin wadannan kudaden ba a lokacin da ya shugabance ta.
Furucin Orji Kalu ya zo ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Legas, yayin gabatar da jawaban kare kai game da tuhumar da hukumar EFCC ta yi ma shi tare da wani kamfanin sa Slok Nigeria Limited, da kuma tsohon Daraktan kudi kuma babban akanta na gwamnatin sa Jones Udeogu.
Bayan janye tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa ta tsawon shekaru 12, Orji Kalu ya ce ko a lokacin da zai sauka daga mulki, sai da su ka ci bashi kafin su iya biyan albashin ma’aikata.
Ya ce dudu-du a lokacin da suka karbi jagorancin jihar a watan Yuni na shekara ta 1999, abin da jihar Abia ke samu daga gwamnatin tarayya a kowane wata bai wuce naira miliyan 168 zuwa 172 ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/libertytvnews
Twitter: https://twitter.com/libertytvnews
Instagram: https://instagram.com/libertytvng
Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/libertyradioabuja
Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?
Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.
Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com
You must log in to post a comment.