Home Labaru Taimakon Da Iran Ke Wa El-Zakzaky A Kan Nijeriya

Taimakon Da Iran Ke Wa El-Zakzaky A Kan Nijeriya

1065
0
Ibraheem El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Shi’a Ta Nijeriya
Ibraheem El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar Shi’a Ta Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi zargin cewa, shugaban kungiyar maniya akidar Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya na da manufar son kafa kasar musulunci a Nijeriya.

Haka kuma, Gwamnatin ta ce malamin ya na da cikakken goyon bayan gwamnatin kasar Iran domin cimma wannan manufa.

Gwamnatin ta yi wannan ikirari ne, a cikin wata takardar rantsuwa ta kotu da ta cike a kan karar kungiyar Shi’a da ke kalubalantan umurnin Babbar Kotun Tarayya na bayyana ta a matsayin haramtacciya.

Mai shari’a Nkeonye Maha, ya tsaida ranar 11 ga watan Satumba domin ci-gaba da sauraren karar da Femi Falana ya shigar a madadin kungiyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com