Home Labaru Ododo Ya Doke Adeyemi Da Sauran Su a Samun Tikitin Apc Na...

Ododo Ya Doke Adeyemi Da Sauran Su a Samun Tikitin Apc Na Zaben Gwamnan Kogi

1
0

Mai binciken kudin kananan hukumomin jihar Kogi Ahmed
Usman Ododo, ya zama dan takarar gwamnan jihr a karkashin
jam’iyyar APC a zaben da zai gudana a watan Nuwamba.

An dai gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar APC ne ta hanyar wakilai a fadin gudunmomin jihar a ranar Juma’a, 14 ga watan Afrilu.

Sakataren kwamitin shirya zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Kogi Patrick Obahiagbon ya sanar da sakamakon a madadin shugaban kwamitin Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Ahmed Usman Ododo dai ya yi nasara a zaben fidda gwanin ne, bayan ya samu jimilar kuri’u dubu 78 da 704, inda ya lallasa sauran ‘yan takara shida da tazara mai yawan gaske.

Daga cikin masu masu neman tikitin takarar dai akwai mataimakin gwamnan jihar Edward Onoja, da shugaban ma’aikatan Gwamna Yahaya Bello, Mohammed Asuku.