Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa a jihar Yobe, ta
ayyana Ibrahim Bomai a matsayin wanda ya lashe zaben
sanatan mazabar Yobe ta Kudu a majalisar dattawa.
Baturen zaben Abatcha Melemi, ya ce Bomai na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 69 da 596, inda ya lallasa abokin karawar sa na jam’iyyar PDP Halilu Mazagane, wanda ya samu kuri’u dubu 68 da 885.
A baya dai hukumar zaben ta dakatar da tattara sakamakon zaben yankin tare da ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba, saboda wasu dalilai na aringizon kuri’u a rumfunan zaben Manawachi a karamar hukumar Fika.
Da ya ke sanar da manema labarai sakamakon zaben, baturen zaben ya ce abin da ya fada gaskiya ne kuma shi ne adalci.
You must log in to post a comment.