Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama, ya koka bisa yadda gwamnati mai ci a karkashin Donald Trump, ta gaza daukar matakai, na tsaurara dokokin sa ido kan mallakar bindiga tsakanin ‘yan kasar.
Karanta Wannan: Ciyar Da Dalibai: Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kwanoni Da Cokula 1,482 Ga ’Yan Firamare A Jigawa
Obama ya bayyana haka, ne yayin tsokaci kan halaka mutane akalla 29 da ‘yan ta’adda suka yi a Ohio, da Dayton, a karshen mako, da kuma karuwar matsalar a sassan kasar.
Tsohon shugaban na Amurka ya ce abin takaice ne cewar yadda Amurka kasa mafi karfi da ci gaba a duniya, ke fama da matsalar marasa tunani, da kuma rashin tsaurara dokokin sa ido wajen mallaka da kuma amfani da bindigogi, duk kuwa da cewar Amurkawa na ci gaba da fuskantar kisan gillar ‘yan ta’adda akai akai.
Jawabin na Barrack Obama, martani ne kan kisan gillar da ‘yan ta’adda suka yiwa mutane 29 a karshen mako, 20 a El-Paso da ke jihar Texas da kuma 9 a Dayton dake jihar Ohio.
You must log in to post a comment.