Home Labaru Kiwon Lafiya EBOLA: Uganda Za Ta Fara Gwajin Sinadaran Rigakafi

EBOLA: Uganda Za Ta Fara Gwajin Sinadaran Rigakafi

254
0

Kasar Uganda ta bayyana fara amfani da gwajin allurar rigakafin cutar Ebola, da za a yi amfani da shi a Jamhuriyar Dimikaradiyar Congo mai makwabtaka da ita, inda annobar ta Ebola ta hallaka mutane dubu 1 da 800 cikin shekara daya.

Karanta Wannan: Kishin Kasa: Buhari Ya Jinjina Wa ‘Yan Nijeriya Bisa Kaurace Wa Zanga-Zangar Juyin-Juya-Hali

Aikin gwajin maganin rigakafin hana kamuwa da annobar ta Ebola MVA-BN da kamfanin hada magunguna na Amruka Johnson & Johnson, ya samar, zai dauki tsawon shekaru 2 ana yi, kamar yadda sanarwar da hukumar binciken magunguna ta kasar Uganda MRC ta sanar.

Hukumar ta MRC ta bayyana cewa tafiyar da aikin bada maganin riga kafin, zai kunshi kimanin jami’an kiyon lafiya dubu 8, wadanda kuma ke sahun gaba a cikin aikin sun hada ne da malaman tsafta, da na motocin daukar marasa lafiya, da kuma masu kula da dakunan ajiye gawarwaki, sai kuma masu binne mamata a lardin Mbarara dake yammacin kasar ta Uganda.

Kawo yanzu dai babu maganin da zai hana kamuwa ko kuma warkar da cutar Ebola a duniya, sai dai ana da kyakkyawan fata samun maganin, ta la’akari da cewa akwai wasu jerin magungunan hana kamuwa da cutar ta Ebola na gwaji da ake kan samarwa.