Home Home NYSC: Mata Za Su Iya Sauya Jiharsu Ta Yi Wa Kasa Hidima...

NYSC: Mata Za Su Iya Sauya Jiharsu Ta Yi Wa Kasa Hidima Ba Tare Da Yin Tafiya Ba

316
0

Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima NYSC, ta sharwaci dalibai mata su je sansanin ta da ke kusa da su da takardun shaidar auren su, da sauran takardun da za su tabbatar da cewa sun yi auren domin a sauya masu jihar yi wa kasa hidima.

Mata da maza matasa dai su na kwashe tsawon shekara daya su na yi wa kasa hidima idan sun kammala karatun digiri ko HND kafin su kai shekaru 30 da haihuwa.

Hukumar NYSC, ta ce matan aure za su iya sauya jihar su ta yi wa kasa hidima ba tare da sun yi wata doguwar tafiya ba.

A wani sako da ta wallafa a shafin ta na Twitter, hukumar ta ce duk masu yi wa kasa hidima da aka tura jihohin da ba nan mazajen su ke zama ba, su garzaya sansanin horar da masu yi wa kasa hidima da ke kusa da su domin a sauya masu jihar da za su yi wa kasa hidima.

Leave a Reply