Home Home ‘AYan Matan Chibok’ 2 Sun Gudo Daga Hannun Boko Haram

‘AYan Matan Chibok’ 2 Sun Gudo Daga Hannun Boko Haram

1
0

Wasu karin ‘yan mata biyu daga cikin daliban Makarantar Sakandaren ‘yan Mata ta garin Chibok a Jihar Borno sun gudo daga hannun mayakan Boko Haram da su ka sace su shekaru tara da su ka gabata.

Majiyoyin tsaro da mazauna Jihar Borno sun shaida wa manema labarai cewa, matan biyu sun samu tserewa ne sakamakon tsananta luguden wuta da sojoji ke yi akan sansanonin kungiyar da ke Dajin Sambisa.

Wata majiyar tsaro ta ce, daliban da su ka gudo sun hada da wata Hauwa Mutah da Esther Markus. Kawo yanzu dai daliban makarantar 96 ne su ka rage a hannun kungiyar Boko Haram, wadda ta sace su tun a watan Afrilu na shekara ta 2014