Home Labaru Nnpp Ba Ta Dan Takarar Gwamnan Kano —Apc Ga Kotu

Nnpp Ba Ta Dan Takarar Gwamnan Kano —Apc Ga Kotu

41
0

Jam’iyyar APC ta bukaci kotu ta soke nasarar Abba Kabir
Yusuf na Jam’iyyar NNPP a zaben Gwamnan Jihar Kano.

APC ta shaida wa Kotun Sauraron Kararrin Zaben Gwamnan jihar Kano cewa, hasali ma Abba Kabir bai cancanci tsayawa takara a zaben ba.

Takardar karar da jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta shigar, ta bayyana cewa babu sunan Abba Kabir a jerin sunayen ‘yan takarar da NNPP ta tura wa Hukumar Zabe ta Kasa, don haka ta bukaci kotun ta ayyana cewa NNPP ba ta dan takara a zaben.

Idan dai ba a manta ba, hukumar zabe ta sanar cewa Abba Kabir ya lashe zaben da kuri’u Miliyan 1 da dubu 19 da 602, yayin da mataimakin gwamnan jihar Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ya zo na biyu da kuri’u dubu 890 da 705.

Sai dai APC ta shaida wa kotun cewa, jam’iyyar NNPP ba ta samu mafi rinjayen kuri’un da za a bayyana dan takarar ta a matsayin wanda ya yi nasara ba, domin a cewar ta, wasu kuri’un da aka kada wa NNPP lalatattu ne, kuma idan aka cire su APC za ta samu rinjayen kuri’un da aka jefa.

Leave a Reply