Home Labaru Sanata Anyanwu Ya Lashe Tikitin Tsayawa Takarar Gwamnan Imo

Sanata Anyanwu Ya Lashe Tikitin Tsayawa Takarar Gwamnan Imo

1
0

Sanata Samuel Anyanwu, ya lashe zaben fidda gwani na
takarar kujerar gwamnan Jihar Imo a karkashin jam’iyyar
PDP da kuri’u 802.

Idan dai za a tunawa, babban abokin karawar sa tsohon gwamnan Jihar Chief Emeka Ihedioha ya janye daga neman tikitin a karkashin jam’iyyar PDP.

Wakilan jam’iyyar 802 da su ka fito daga kananan hukumomi 27 ne su ka zabi Sanata Anyanwu, yayin da sauran ‘yan takarar su ka samu kuri’u 23, sannan kuri’u 28 su ka kasance marasa kyau.

Shugaban kwamitin zaben Kenneth Okon, da sakataren kwamitin Olalekan Rotimi ne su ka ayyana Sanata Anyanwu a matsayin wanda ya lashe zaben, tare da samun tabbacin shugaban jam’iyyar na jihar Injiniya Charles Ugwu.

Sanata Samuel Anyanwu, ya nuna matukar godiya bisa yadda wakilan jam’iyyar su ka yi ma shi ruwan kuri’u, sannan ya bukaci al’ummar jihar su fito su zabi PDP yayin zaben da ke tafe.