Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC ta ce za ta sake komawa ga gwamnatin tarayya domin ta ji yadda ma’aikata za su rayu bayan sake kara farashin man fetur a kasa.
Ƙungiyar wadda ta bayyana hakan a ranar Alhamis, ta ce farashin mai a yanzu haka ya riga ya haɗiye sabon tsarin albashin da gwamnati ta yi alƙawarin bayarwa na naira dubu 70 wanda kuma har yanzu ba a fara bayarwa ba.
Shugaban ƙungiyar ta NLC, Kwamared Joe Ajaero wanda ya bayyana hakan yayin buɗe wani taron ƙarawa juna sani a Legas ya ce gwamnati ta yaudare su ta hanyar amince wa da naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.
Ya kuma shawarci gwamnati ta magance matsalar yunwa da talauci da damuwar da ƴan Najeriya ke fama da ita tun kafin al’amura su fi ƙarfin su.