Home Labaru Ilimi Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Bukatar Sa Almajirai A Tsarin Ilimin...

Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Bukatar Sa Almajirai A Tsarin Ilimin Boko

748
0

Majalisar wakilai ta ki amincewa da kudurin sanya almajiranci a cikin tsarin Hukumar bada ilimin bai-daya UBE, wadda ke karkashin Ma’aikatar Ilimi ta kasa.

An dai gabatar wa majalisar bukatar ne a cikin wani kuduri mai kunshe da abubuwa goma.

Taken kudurin kuwa shi ne ‘Kawar da Almajirai daga kan tituna ta hanyar samar da Ilimi mai nagarta domin inganta rayuwar su.’

Mansur Soro, da Ibrahim Umar da Sa’idu Abdullahi ne su ka dauki dauyin gabatar da kudurin, sai dai bukatar neman a sa Almajirai a cikin tsarin hukumar bada ilimi na bai-daya ba ta samu karbuwa ba.

Majalisar dai ta aminta da sauran kudurorin tara, wadanda su ka shafi kawar da barace-barace, inda su ka yi kira ga gwamnatoci su tabbatar da an bi dokar.

Haka kuma, Majalisar ta yi kira ga jihohin da matsalar bara ta shafa su dage wajen tabbatar da yara ‘yan tsakanin shekaru 6 zuwa 16 an tura su makarantu domin koyon ilimin da ake badawa kyauta a karkashin dokar UBEC.