Home Labarai Nijeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 1.5 Saboda Fasa Bututun Mai –...

Nijeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 1.5 Saboda Fasa Bututun Mai – NNPC

13
0

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPC Mele Kyari,
ya koka da yadda ayyukan tsageru masu fasa bututun Mai da
masu haramtattun matatu ke haifar da tarin matsaloli a kasar
nan.

Da ya ke jawabi a gaban kwamitin man fetur na majalisar
wakilai, Mele Kyari ya ce hakan ya janyo asarar dala biliyan
daya da rabi na danyen mai daga watan Janairu zuwa yau.

Jami’in, ya ce bangaren man fetur ya na samar da mafi karancin
danyen man da ya kai ganga miliyan 1 da dubu 49 a kowace
rana, sakamakon karuwar ayyukan barna da masu gudanar da
haramtattun matatu.