Home Labaru Ilimi Watanni 10 Har Yanzu Wasu ‘Yan Mata Su Na Hannun ‘Yan Bindiga

Watanni 10 Har Yanzu Wasu ‘Yan Mata Su Na Hannun ‘Yan Bindiga

39
0

Nan da kwanaki 10 masu zuwa, ‘yan matan makaratar
sakandaren gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri a jihar Kebbi za
su cika watanni 10 a hannun ‘yan bindiga, biyo bayan sace su da kasurgumin dan bindiga Dog Gide ya yi.

A ranar 17 ga watan Yuni shekarar da ta gabata ne, ‘yan bindiga
su ka yi awon gaba da gwamman dalibai da malamai biyar daga
makarantar.

Sai dai duk da biyan kudin fansa da musayar fursunoni da aka yi
a lokuta dabam-dabam, har yanzu ‘yan mata 11 su na hannun
‘yan bindigar.

A baya dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, akalla mata 13
da ake garkuwa da su ne aka daura ma aure da ‘yan bindigar,
kuma har wasu daga cikin su sun samu juna biyu.