Home Labarai Magori: ‘Yan Nijeriya Za Su Zabi APC a 2023 Saboda Ta Yi...

Magori: ‘Yan Nijeriya Za Su Zabi APC a 2023 Saboda Ta Yi Namijin Kokari – Buhari

541
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin APC ta yi
wa ‘yan Nijeriya namijin kokarin da ya cancanci su sake zaben
ta.

Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi aiki mai kyau, musamman a
bangaren aikin noma da gina tituna da ilmin fasahar zamani da
jin dadin ‘yan Nijeriya.

Shugaba Buhari ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, zai cigaba
da karfafa dimokradiyya a siyasa da jagoranci.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin sabon
shugaban jam’iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu a fdadar sa
da ke Abuja.

Ya ce ya kamata su yi farin ciki jam’iyyar su ta dinke barakar ta,
domin fuskantar kalubalen da ke gaban su na zaben jihohi da na
tarayya.

Leave a Reply