Home Labarai Nijeriya Ta Biya Diyyar Miliyan 289 Ga Wadanda ’Yan Sandan SARS Suka Ci Zarafin...

Nijeriya Ta Biya Diyyar Miliyan 289 Ga Wadanda ’Yan Sandan SARS Suka Ci Zarafin Su

30
0

Gwamnatin tarayya, ta biya ‘yan Nijeriya 74 da aka tabbatar jami’an ‘yan Sanda bangaren masu yaki da ‘yan fashi da makami da aka rusa ta SARS, sun ci zarafin su diyyar naira Naira miliyan 289.

Shugabar Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa Dr Salamatu Suleiman ta gabatar da kudaden ga mutanen 74, inda ta ce kafin nan an biya wasu 94 naira miliyan 431.

Salamatu Suleiman, ta gode ma wadanda su ka gabatar da korafi a gaban kwamitin bincike na musamman da gwamnati ta kafa, domin bin Kadin wadanda jami’an ‘yan sandan su ka ci zarafin su ta hanyar doka.

Majalisar gudanarwa ta hukumar ta sha alwashin aiwatar da dokokin da aka kafa ta a kai, na bin kadin hakkin wadanda aka ci zarafin su a kowane bangare.