Home Labarai Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Ghali Na Abba Ya Koma PDP

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Ghali Na Abba Ya Koma PDP

36
0

Tsohon kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na’Abba, ya sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar PDP.

Ghali Na’Abba,yace jam’iyyar APC da ya shiga shekaru biyu da su ka gabata, annoba ce kuma masifa ce da ta maida Nijeriya baya.

Ya ce tabbas APC za ta girbi abin da ta shuka, domin za ta haɗu da fushin ‘yan Nijeriya a zaben shekara ta 2023 saboda ta jefa ƙasar nan cikin mawuyacin hali.

An dai sanar da sauya shekar Ghali Na’Abba ne a wajen taron tsofaffin ‘yan majalisar wakilai da ya gudana a Abuja, a karkashin jagorancin tsohon mataimakin Kakakin sa Austin Okpara.

Ya ce Ghali Na’abba tare da ɗumbin magoya bayan sa a jihar Kano da sauran jihohin Nijeriya, sun koma jam’iyyar PDP domim su bada gudummuwar ɗora Atiku Abubakar a kan madafun iko a shekara ta 2023.