Hukumar yaki da cin hanci da almundahana ICPC, ta ce ta gano ayyukan mazabu da aka karkatar a fadin Nijeriya, wadanda kudin su ya kai Naira biliyan 2 da miliyan 800.
ICPC, ta ce ta gano hakan ne ta hanyar wani kwamiti da ta kafa domin bin diddigin ayyukan mazabu a fadin Nijeriya.
Wanda ya gano ayyukan mazabu kusan 2,444 da aka karkatar da kudinsu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.
Yayin da ya ke gabatar da takaitaccen kundin binciken hukumar a Legas, daraktan gudanarwa na hukumar Akeem Lawal, ya ce a karon farko an gano ayyukan mazabu 524 a jihohi 12 da birnin tarayya Abuja a shekara ta 2019.
Sannan a karo na biyu, kwamitin bin diddigin ya gano ayyukan mazabu 822 a jihohi 16 a shekara ta 2020, yayin da a karo na uku na bin diddigin an zakulo ayyukan mazabu dubu 1 da 98 a jihohi 17 da birnin tarayya Abuja.
You must log in to post a comment.