Home Labaru Leicester Ta Lallasa Manchester United Da Ci 4-2

Leicester Ta Lallasa Manchester United Da Ci 4-2

14
0

Kungiyar Leicester ta lallasa Manchester United da ci 4-2 a gasar Firimiya ta kasar Ingila da aka kara yau asabar, abinda ya baiwa Leicester damar matsawa gaba a teburin gasar.

Greenwood ya fara jefawa Manchester United kwallo a minti 19 da fara wasan, yayin da Tielemans ya farkewa kungiyar sa ta Leicester a minti 31, inda aka tafi hutun rabin lokaci ana 1-1.

Da aka dawo hutun rabin lokaci, Soyuncu ya jefawa Leicester kwallon ta na 2 a minti 78, sai kuma Marcus Rashford ya farke a minti 82, kafin Jemie Vardy ya jefa ta 3 bayan minti guda.

A minti 90 Daka ya jefa kwallo ta 4 abinda ya sa aka tashi wasan Leicester na da ci 4-2.