Home Labarai Nigeria: Pengassan Ta Zargi Sojoji Da Hannu A Satar Danyen Mai A Kasar

Nigeria: Pengassan Ta Zargi Sojoji Da Hannu A Satar Danyen Mai A Kasar

27
0

Kungiyar manyan ma’aikatan bangaren man fetur da iskar gas ta Nijeriya PENGASSAN, ta zargi sojoji da kasancewa ummul’haba’isin yawaitar satar danyen mai a Nijeriya.

Shugaban kungiyar na kasa Festus Osifo, ya ce jami’an sojin da aka ba aikin kare butatun mai ne su ke hadin baki da bata-gari ana satar man, ta fuskar bada kariya ga barayin da masu gudanar da kananan matatun mai.

Osifo ya yi zargin cewa, ana yin satar ne da sanin hukumomin da aka dora wa alhakin kula da da kadarorin man Nijeriya.

Ya ce bangaren sojojin da ke aikin tsaron ruwan Nijeriya na Amphibious Brigade, da takwarorin su na sojin ruwa da ke Fatakwal da wasu manyan jami’an soji su na da hannu dumu-dumu a wannan danyen aiki na satar danyen mai.

Festus Osifo, ya ce bincike ya nuna cewa, har ma ja’ami’an soji su na bada cin hanci ga manyan su, domin kawai a tura su aiki a wuraren da ake tafka badakalar a yankin Neja Delta.