Home Labaru Niger Delta: An Sake Yin Garkuwa Da Wasu Turawa Biyu

Niger Delta: An Sake Yin Garkuwa Da Wasu Turawa Biyu

510
0

Masu garkuwa da mutane sun sace wasu Turawa biyu dake aiki a wani kamfanin Mai dake garin Abuja na karamar hukumar Ahoada dake yamma a jihar Rivers.

Mai magana da yawun rundunar  tsaro ta JTF a yankin Niger Delta, , Manjo Ibrahim Abdullahi, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da manema labarai  a yankin.

Ya ce ‘yan bindigar sun sake yin awon gaba da wasu Turawa biyu, dake aiki a kamfanin ta ce Mai na Niger Delta Petroleum Resources da ake kira NDEP a takaice a garin Abua.

‘Yan bindigar dai sun kutsa ne a yankin da ya ratsa ta cikin kamfanin, inda nan take su ka yi gaba da ma’aikatan kamfanin biyu, bayan da suka sami labari, sun bi sahun ‘yan bidigar sai dai ba su yi nasara ba.

Haka kuma rundunar JTF ta ba kamfanin shawarar ya samar da tsaro a inda yake gudanar da aikinsa, domin kare ma’aikata da dukiyarsa.

Lamarin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ya sake dawowa gadan-gadan a yankin Niger-Delta mai arzikin Mai.