Home Labaru Ni Ba Ƙaramin Ƙwaron Da APC Za Ta Yi Wa Barazana Da...

Ni Ba Ƙaramin Ƙwaron Da APC Za Ta Yi Wa Barazana Da Kora Ba Ne – Marafa

67
0

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Kabiru Marafa, ya ce barazanar korar shi daga jam’iyyar APC shirme ne, kuma shi ba ƙaramin ƙwaron dan siyasar da jam’iyyar za ta iya yi wa barazana ba ne.

Kabiru Marafa, ya ce idan ma an kore daga APC ba shi ne zai magance matsalar jam’iyyar ba, illa ma ya ƙara rura wutar rikici fiye da ta yanzu.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, Marafa ya ce Gwamna Mala Buni bai cancanci riƙe jam’iyyar APC ba, tunda a gefe ɗaya ya na riƙe da kujerar gwamnan Jihar Yobe.

Marafa ya kara da cewa, Kwamitin Mai Mala Buni haramtacce ne, don haka ba zai iya shirya wani taro ko zaɓen fidda gwani ko wani abu a bisa doka ba   .