Home Labaru Amurka Ta Cire Nijeriya Daga Jerin Kasashen Da Ke Hana Addini

Amurka Ta Cire Nijeriya Daga Jerin Kasashen Da Ke Hana Addini

13
0

Kasar Amurka ta sa sunan Rasha a jerin kasashen duniya da ke hana jama’a gudanar da ’yancin addinin da su ke so, yayin da ta cire sunan Nijeriya da ta sanya a shekarar da ta gabata.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce ya sa Rasha cikin jerin kasashen ne saboda rawar da ta ke takawa wajen tursasa wa mabiya wasu addinai da kuma hana su gudanar da ibadar su.

Sauran kasashen da ke cikin jerin sun hada da China da Myanmar da Eritrea da Iran da Koriya ta Arewa da Pakistan da Saudi Arabia da Tajikistan da kuma Turkmenistan.

Antony Blinken, ya ce Amurka ba za ta kauda ido daga hakkin da rataya a kan ta na tabbatar da ‘yancin addini da kuma ba jama’a damar gudanar da ibadar su kamar yadda su ke so ba.

Ya ce yanzu haka ya fara ziyarar wasu kasashen Afirka, inda ya sauka a kasar Kenya kafin ya je kasashen Nijeriya da Senegal domin jaddada matsayin gwamnatin Amurka a kan dimokiradiya da kuma kare hakkin Bil-Adama.