Home Labaru Nemin Mafita: Shugabannin Kudu Da Tsakiya Sun Bijire Wa Gayyar Janar Abdussalami

Nemin Mafita: Shugabannin Kudu Da Tsakiya Sun Bijire Wa Gayyar Janar Abdussalami

397
0

Shugabannin al’ummomin kudu da yankin arewa ta tsakiya, sun bijire wa gayyatar da tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar ya yi masu, domin halartar wani taron tattaunawa a kan al’amurran da su ka shafi kasa da tsaro da aka shirya gudanarwa a birnin Minna na Jihar Neja.

Jiga-jigan yankunan biyu dai sun ki amincewa da gayyatar ne, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere Ayo Adebanjo, da shugaban kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Chief John Nwodo, da kuma shugaban al’ummomin yankin Arewa ta tsakiya Dakta Pogu Bitrus.

Dukkan shugabannin yankunan biyu sun bijire wa gayyatar ne saboda an gayyaci kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, lamarin da su ka bayyana a matsayin cin fuska a wajen su.

Shugabannin sun ce, sun aminta da duk bangarorin da aka gayyata zuwa wajen taron, amma ba su gamsu da kungiyoyin Fulani da su ka yi kaurin suna wajen tada zaune tsaye a Nijeriya ba.