Home Labaru Jerin Ministoci: Abin Da Ya Sa Aka Cire Sunan Akinwunmi Ambode

Jerin Ministoci: Abin Da Ya Sa Aka Cire Sunan Akinwunmi Ambode

471
0

Tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jerin sunayen mutane 42 da ya ke son ba mukamin minista ake mamakin rashin ganin sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a ciki.

Daga cikin mutanen da ake mamakin rashin ganin sunan su kuwa akwai tsohon gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, musamman ganin ya na da tudun dafawa a fadar shugaban kasa.

Wata majiyar daga fadar shugaban kasa ta ce, dole ce ta sa shugaba Buhari ajiye sunan Ambode, domin nada shi a matsayin minsta zai janyo baraka tsakanin shugaba Buhari da wasu sahiban sa daga jihar Legas.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Duk dalilan da su ka tilasta shugaba Buhari fasa ba Ambode minista su na da alaka da Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kasance dan siyasa mafi karfi a tsakanin al’ummomin kabilar Yarbawa.