Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyar PDP mai hamayya ta mutu a fagen siyasar ƙasa
Yayin da yake jawabi a ofishin jam’iyyar NNPP na jihar Katsina jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam’iyyar APC ta jefa kanta cikin abin da ya kira ”halaka”.
Ya karada cewa jam’iyyar PDP dama kowa ya sani a yanzu dai matacciya ce, inda ya kara da cewa ada can baya yana cikinta, kuma tun da ta saki layi suka sake.
Ya kuma zargi jagororin gwamnatin APC da nuna halin ko- in- kula game da halin da ƙasa ke ciki, musamman ta fuskar matsalar rashin tsaro.
Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira ga talakawan Najeriya su kauce wa karɓar taliya ko wasu kuɗi da ya ce ba su taka kara suka karya ba a ranar zaɓe domin sarayar da haƙƙoƙinsu.