Home Labaru Neman Sulhu: Gwamna Ya Gwangwaje Mbaka Da Naira Milliyan 30, Doya 200,...

Neman Sulhu: Gwamna Ya Gwangwaje Mbaka Da Naira Milliyan 30, Doya 200, Don Ya Daina Sukar Buhari

79
0

Gwamnan  jihar Ebonyi Dave Umahi, ya yi kira ga daraktan Adoration Ministry Enugu, Rabaren Father Ejike Mbaka ya daina sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamna Dave Umahi, ya yi wannan kiran ne yayin bikin girbi na wannan shekarar tare da nuna godiya ga shugaba Father Ejike Mbaka.

Umahi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, ya samu rakiyar Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Umahi, ya bada naira miliyan talatin, da Doya guda dari biyu da kuma buhunan shinkafa kuma ya sanar da cewa shugaban kasa Buhari na aiki wurin gyara tattalin arzikin kasar nan tare da rage fatara a Najeriya.

Gwamna Umahi  ya ce gwamnonin yankin da kuma kungiyar Ohanaeze Ndigbo da sauran fitattun jama’ar yankin suna kokarin ganin a sako shugaban ‘yan awaren masu kafa kasar Biafra, Mazi Nnamdi Kanu nan babu dadewa.

Ya ce babu shakka Mbaka ya goyi bayan Buhari a yayin gangamin neman zabensa karo na farko, sai dai daga baya ya fara sukar shugaban kasa kan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.