Home Labaru Shugaba Buhari Ya Yiwa Al’Ummar Najeriya Addu’ar Samun Zaman Lafiya

Shugaba Buhari Ya Yiwa Al’Ummar Najeriya Addu’ar Samun Zaman Lafiya

20
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shafe tsawon lokaci yana yi wa al’ummar kasar nan Addu’ar samun zaman lafiya a Masallacin Ka’aba da ke Saudiya, inda ya gudanar da aikin ibadar Umrah.

Mai magana da yawun Buhari Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, shugaba Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da Al’umma addu’ar maido da zaman lafiya da tsaro a kasar nan da sauran kasashen duniya.

Har ila yau shugaban ya yi addu’ar farfadowar tattalin arzikin Najeriya wanda annobar Korona ta yi wa illa.

Kazalika Shehu ya ce, shugaba Buhari tare da mataimakin gwamnan Madinah, Yarima Sa’ud Al-Faisal sun shafe tsawon lokaci a cikin Masallacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam, suna Addu’o’i.

A ranar Litinin da ta gabata ne, shugaba Buhari ya bar Abuja domin halarttar taron zuba jari  karo na biyar da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudiya.