Home Labaru Rikicin Siyasar Kano: Ahmadu Haruna Zago: Ya Ce Babu Gudu Ba Ja Da...

Rikicin Siyasar Kano: Ahmadu Haruna Zago: Ya Ce Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Shugabancin Apc

14
0

Mutumin da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya zaɓa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano ya ce shi ne halattaccen shugaban jam’iyyar duk da kwamitin uwar jam’iyyar na sauraron korafin zaɓe ya fito fili ya ayyana Abdullahi Abbas na ɓangaren gwamna Ganduje a matsayin shugaban jam`iyyar.

Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya shaida wa BBC cewa babu abin da ya sha musu kai da aikin kwamitin sauraron korafin zaben, saboda zaben da suka yi sahihi ne.

Wannan iƙirarin dai ya ƙara fito da darewar jam`iyyar APC mai mulki a Kano, ɗaya daga cikin jihohin da ke da tasiri a siyasar Najeriya inda mutum biyu ke ikirarin kujerar shugabancin jam`iyyar a jihar.

Ɓangarorin biyu dukkaninsu sun gudanar da zaɓukan shugabancin jam’iyyar ne daban-daban.

Kuma ayyana Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC a Kano da uwar kwamitin uwar jam’iyyar ya yi ya nuna cewa zaben ɓangaren su Haruna Zago akwai ƙila wa ƙala.

Amma Haruna Zago ya ce sun bi ka’idar zaɓen shugabancin APC kan tsarin yin maslaha ko zaben kai tsaye ko na deleget.

A cewarsa ana maslaha ga waɗanda suka sayi fom suka biya kudi a uwar jam’iyya, suka cike fom suka mayar su suke da hakki a cikinsu su daidata.