Home Labaru Neman Mafita: Matsalar Zamfara Ta Fi Karfin Jami’an Tsaro Kadai – Marafa

Neman Mafita: Matsalar Zamfara Ta Fi Karfin Jami’an Tsaro Kadai – Marafa

202
0

Dan majalisar dattawa Sanata Kabiru Marafa, ya ce jami’an tsaron Nijeriya kadai ba za su iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar Zamfara ba.

Sanata Kabiru Marafa, ya ce saboda yadda matsalar ‘yan bindiga ta satar shanu da kashe jama’a da kuma sace mutane ta yi muni, dole jami’an tsaro su na bukatar tallafin jama’a.

Ya ce duk wanda zai bada labarin halin da mutanen Zamfara ke ciki, ba zai kai jama’ar ke wajen ba matukar ba ya je da kan sa ya gani ba, domin kusan kashi 75 cikin 100 na mazaje a jihar ba sa kwana a gidajen su idan dare ya yi.

Marafa ya cigaba da cewa, a duk lokacin da aka ce an gama sallolin Magriba da Isha’i, abin da kawai namiji zai yi shi ne ya dauki dan makamin sa, wasu su haye saman ita ce wasu kuma su shiga wasu gine-gine su na gadin garuruwan su.’

Sai dai ya ce hakan ba ya na nufin mutane sun dawo daga rakiyar jami’an tsaro ne ba, illa dai jami’an tsaron ba su da yawan da za a ce sun iya samar da tsaro a ko ina, don haka akwai bukatar jama’a su tashi tsaye domin bada gudunmawa wajen kare dukiya da rayukan su.