Home Labaru Kaddara: Yadda Dandazon Kudan Zuma Ya Kashe Wani Jami’in Kwastan A...

Kaddara: Yadda Dandazon Kudan Zuma Ya Kashe Wani Jami’in Kwastan A Legas

357
0

Hukumar yaki da fasa kwauri ta Nijeriya, ta bada sanarwar mutuwar wani babban jami’in ta da ya rasa ran sa sakamakon harbin kudan zuma.

Abubakar Abba dai ya rasa ran sa ne a lokacin da wani dandazon kudan zuma ya baibaye shi, yayin da ya ke sintiri a dajin Ashipa da ke kan iyakar Seme da ke yankin Badagry a Legas.

A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar  Kwastan na Seme Sa’idu Abdullahi ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata, a lokacin da Abba ya ke bakin aikin sa na sintiri.

Hukumar, ta kuma nuna takaicin rashin Abba, wanda ta nuna cewa hazikin jami’i ne da bai taba fashin zuwa aiki ba.

Tuni dai an yi wa gawar sa sutura, an kuma rufe shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada.