Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya karin bayani a kan yadda bashin da ake bin Nijeriya ya karu a karkashin gwamnatin sa.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya ce bashin da ake bin Nijeriya ya karu daga Naira Tiriliyan 12 da biliyan 12 zuwa Naira Tiriliyan 24 da biliyan 387 tsakanin shekara ta 2015 zuwa ta 2018.
Ologbondiyan, ya ce gwamnatin Buhari ta buge da cin bashi na babu gaira babu dalili, inda bashin da ke kan Nijeriya ya karu da kusan Tiriliyan 12 daga shekara ta 2015.
A cewar sa, an yi amfani da kudaden ne wajen yi wa jam’iyyar APC yakin neman zaben da ya gabata, ya na mai zargin gwamnatin APC da karkatar da sama da naira Tiriliyan 1 da biliyan 4 wajen biyan kudin tallafin man fetur.
Jam’iyyar PDP ta cigaba da cewa, duk da irin wannan zargin badakala, ba a ma maganar Naira Tiriliyan 9 da ake tunanin an wawure daga asusun kamfanin NNPC, don haka ya nemi majalisar tarayya ta gudanar da bincike a kan lamarin.