Home Labaru Ilimi Kwarewa: Ganduje Zai Fara Koyarwa A Wata Jami’ar Amurka

Kwarewa: Ganduje Zai Fara Koyarwa A Wata Jami’ar Amurka

475
0

Jami’ar East Carolina da ke Amurka ta ba Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matsayin Farfesa sakamakon abin da ta kira ƙwarewar sa wurin gudanar da mulki na gari da kuma inganta rayuwar al’umma.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na jihar, Abba Anwar ya fitar, gwamnan zai fara bayar da shawarwari ga ɗalibai masu digiri na uku, da kuma ƙananan malamai.

Haka kuma gwamnan zai shige gaba wurin ba cibiyar biincike ta jami’ar shawarwari kan batutuwan ilimi da kuma gudanar da gwamnati ta intanet da kuma harkokin ƙasa da ƙasa.