Home Labaru NEITI Ta Nemi A Binciki Yadda Tetfund Ta Kashe Naira Tiriliyan 1

NEITI Ta Nemi A Binciki Yadda Tetfund Ta Kashe Naira Tiriliyan 1

242
0
Kungiyar rajin Sa-Ido A Kan Yadda Ake Kashe Kudaden Ayyukan Gwamnati, NEITI
Kungiyar rajin Sa-Ido A Kan Yadda Ake Kashe Kudaden Ayyukan Gwamnati, NEITI

Kungiyar rajin sa-ido a kan yadda ake kashe kudaden ayyukan gwamnati NEITI, ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta gudanar da binciken yadda Hukumar Inganta Manyan Makarantu TETFUND ta kashe naira biliyan 999 da miliyan 3 a cikin shekarun 2012 zuwa 2016.

Hukumar NEITI, ta ce ta gano TETFUND ba ta da wani takamaimai ko tartibin jadawalin kididdigar yadda ake kashe kudaden gudanar da ayyuka.

Sai dai hukumar TETFUND ta karyata dukkan zarge-zargen da NEITI ta yi ma ta, inda ta ce Asusun Gwamnatin Tarayya ya ba  ta naira biliyan 804 da miliyan 9 ne daga shekara ta 2012 zuwa 2015 daga harajin da aka karba na kamfanonin albarkatun kasa, sannan an ba ta naira biliyan 188 da miliyan 3 daga harajin kamfanonin da ba na albarkatun kasa ba.

Damuwar da hukumar NEITI ta nuna dai ita ce, duk wani kokari da ta yi domin hukumar TETFUND ta ba ta kwafen jadawalin kudaden da ake kashewa ko na aikin da aka yi ya ci tura.