Home Labaru Akwai Masu Kokarin Janyo Wa APC Da Gwamnati Na Matsala Daga Abuja...

Akwai Masu Kokarin Janyo Wa APC Da Gwamnati Na Matsala Daga Abuja – Masari

202
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamna jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi zargin cewa akwai wasu ‘yan siyasar Katsina da ke Abuja, wadanda ke amfani da karfin gwamnatin tarayya domin janyo wa jam’iyyar APC matsala a jihar sa.

Masari ya ce mutanen da ke buga siyasar su a wajen jihar, su na kokarin jefa jam’iyyar APC da gwamnatin sa cikin wani hali a Katsina.

Gwamnan ya bayyana haka ne, yayin da ya gana da shugabannin jam’iyyar APC daga kananan hukumomi 34 na jihar Katsina a karshen makon da ya gabata.

Ya ce jam’iyyar APC ta na bukatar garambawul domin abubuwa su mike, ya na mai cewa rashin bin doka da oda na iya kawo karshen jam’iyyar APC.

Gwamnan ya cigaba da cewa, ana amfani da kudin gwamnatin tarayya wajen yakar su, kuma sun san abubuwan da ke faruwa.

A karshe ya ce, wadanda su ka fadi zaben fidda da gwani a shekara ta 2015 har yau ba su shiga cikin Katsina ba, don haka ya ce ba za su bari su janyo matsala a siyarsa da mulkin jihar Katsina ba.