Home Labaru NDLEA Ta Kama Masu Safarar Miyagun Kwayoyi 15 A Jihar Gombe

NDLEA Ta Kama Masu Safarar Miyagun Kwayoyi 15 A Jihar Gombe

188
0

Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Gombe, ta ce ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 15 tsakanin watannin Janairu zuwa Satumba.

Shugaban hukumar Aliyu Adole ya bayyana haka, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a garin Gombe.

Ya ce hukumar ta kama mutanen ne da kilogram 523 da 174 na miyagun kwayoyi, wanda a ciki akwai ganyen tabar wiwi.

Adole ya kara da cewa, abin takaici ne yadda mutane musamman matsasa su ka koma ga noman ganyen tabar wiwi maimakon kayan abinci.

A karshe ya bukaci masu ruwa da tsaki da malaman adini, su hada hannu da hukumar don ganin an wayar da kan matasa ilollin da ke tattare da yin tu’amalli da miyagun kwayoyi.