Home Labaru Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Lalong Na Jam’iyyar APC

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Lalong Na Jam’iyyar APC

219
0
Simon Lalong, Gwamnar Jihar Filato

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Filato da ke zama a Jos, ta tabbatar da sake samun nasarar gwamnan jihar Simon Lalong a zaben shekara ta 2019.

Jam’iyyar PDP da dan takarar Jeremiah Useni dai sun garzaya kotun ne domin neman ta soke zaben gwamna Lalon bisa zargin an tafka masu magudi.

Kafin kotun ta zartar da da hukuncin, dararuruwan magoya bayan Simon Lalong da abokin hammayar sa Sanata Jeremiah Useni na jam’iyyar PDP sun mamaye harabar kotun, inda Mai shari’a H.A. Saleeman ke jagorantar lauyoyin da su ke yanke hukuncin.

Sanata Jeremiah Useni, ya shigar da karar kallubalantar nasarar gwamna Lalong, inda ya yi ikirarin cewa an soke kuri’u a bangarorin da PDP ke da rinjaye, don haka ya ce Lalong bai cancanci ya tsaya takara ba.