Home Labarai NDLEA Ta Ce Ta Kama Sarauniyar Ƙwaya a Jihar Taraba

NDLEA Ta Ce Ta Kama Sarauniyar Ƙwaya a Jihar Taraba

72
0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya
NDLEA, ta ce ta kama wata mata da ta kira ‘Sarauniyar Ƙwaya’
a Jihar Taraba, sakamakon zargin ta da tu’ammali da tabar wiwi.

A wata Sanarwa da hukumar NDLEA ta fitar, ta ce jami’an ta
sun kama Lami Mai Rigima a Ƙaramar Hukumar Ardo Kola a
ranar Litinin da ta gabata.

Hukumar NDLEA, ta ce ta fara neman Lami ne tun daga Oktoba
na shekara ta 2021, lokacin da aka kama wani mai suna
Abdullahi Madaki.

An dai kama sarauniyar ne dauke da tabar wiwi da ta kai nauyin
kilo gram 150, sannan hukumar ta kama wani Emeka Okiru bisa
zargin mallakar ƙwayar Tramadol dubu 32 da 700 duk a jihar
Adamawa.