Home Labaru NBC: Kotu Ta Bukaci ICPC Ta Kawo Mata Lai Mohammed

NBC: Kotu Ta Bukaci ICPC Ta Kawo Mata Lai Mohammed

330
0
Lai Mohammed, Ministan Labarai Da Al’adu

Wata kotun tarayya da ke Abuja, ta yi wa Hukumar yaki da rashawa ICPC gargadin karshe, cewa ta kai Ministan yada labarai Lai Mohammed kotu, domin ya bada shaida a kan shari’ar shugaban hukumar kula da kafafen yada labarai NBC, Ishaq Moddibo Kawu, da wasu mutane biyu da ake zargin sun karkatar da Naira biliyan 2 da rabi, wadanda gwamnati ta ware domin sauya hanyoyin sadarwa zuwa na zamani.

Mai shari’a Folashade Ogunbanjo-Giwa, ya ce ministan da wasu mutane biyu su ne sauran shaidu biyu da ba su hallarci kotun a kan shari’ar Kawu da kamfanin Pinnacle, da Lucky Omoluwa da Dipo Onifade ba.

Alkalin ya yi gargadin cewa, idan hukumar ICPC ta gaza kai ministan da wani dan canji da bai hallarci kotun a baya ba hakan kotun za ta iya yin  watsi da karar.

A baya da lauyan masu kara Ephraim Otti ya shaida wa kotun cewa, dan canjin ba ya Nijeriya, sannan ministan ba zai samu damar zuwa kotun ba.