Home Labaru Kalaman Zargi: Sanata Gaya Ya Yi Wa Junaid Muhammad Raddi

Kalaman Zargi: Sanata Gaya Ya Yi Wa Junaid Muhammad Raddi

338
0
Sanata Kabiru Gaya

Sanata Kabiru Gaya, ya bukaci mataimakin Shugaban kasa Yem Osinbajo ya yi watsi da zargin tsohon dan majalisa Junaid Mohammed cewa ya na nuna son kai.

Kabiru Gaya ya bayyana haka ne, bayan wata ganawar sirri da ya yi da Osinbajo a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, inda ya bukaci Junaid Mohammed da ya rika tauna Magana kafin ya furta ta.

Rahotanni sun ce, a baya Junaid Mohammed ya yi zargin cewa, mafi akasarin mutanen da Osinbajo ya ba mukami sun fito ne daga kabilar sa da kuma ‘yan cocin sa.

Sana Gaya ya cigaba da cewa, Shugaban kasa da mataimakin shi sun cancanci mutuntawa daga dukkan ‘yan Nijeriya.

Ya ce ya kamata Junaid ya duba tarihin wadanda ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa kafin ya furta irin adannan kalamai.