Home Labaru Nazari: Akalla Mutane Miliyan 4 Ne Ke Fama Da Bakin Talauci A...

Nazari: Akalla Mutane Miliyan 4 Ne Ke Fama Da Bakin Talauci A Jihar Kano – Sagagi

179
0

Shugaban sashen kasuwanci na makarantar koyon kasuwanci ta Dangote da ke jami’ar Bayero ta Kano Murtala Sagagi, ya ce akalla mutane miliyan 4 ke fama da matsanancin talauci a fadin jihar Kano.

Sagagi ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen taron kungiyar masu ruwa da tsaki na jihar Kano da ya gudana ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce rashin maida hankali wajen farfadowa, tare da gina ayyukan ci-gaba a jihar da gwamnatocin baya basu yi ba, hakan ya sa aka kasa warware wannan matsala da ta dabaibaye mutanen jihar Kano ta bakin talauci.

Sagagi ya cigaba da cewa, akalla masana’antu 500 ne su ka durkushe a jihar Kano, saboda rashin samar da manufofin da za su taimaka wa jihar wajen farfado da irin wadannan kamfanoni. Ya ce har yanzu kuma gwamnatin jihar Kano ba ta iya saita harkokin ayyukan gona ba, ta yadda za a iya samun waraka a fadin jihar.