Hukumar Tsaro ta Sojojin Sama na Nijeriya, ta bayyana kafa kwamitin binciken zargin da Sarakunan Gargajiya na Jihar Zamfara su ka yi cewa sojoji sun kashe fararen hula da ba su ji ba su gani ba.
Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin Vice Marshal Idi Lubo, ya isa Jihar Zamfara tun a ranar Juma’ar da ta gabata.
An dai yi zargin kashe jama’a ne a hare-haren da sojojin sama su ka kai wasu wurare da nufin kakkabe ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar Zamfara.
Da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau a Helkwatar Sojojin, Lubo ya ce Hafsan Hafsoshin Sojan Sama Air Marshall Sadique Abubakar ya damu kwarai a kan wannan zargi da aka yi wa sojojin sama. Ya ce baya ga matukar nuna damuwa da su ka yi, kasancewar su wadanda aka dora ma nauyi da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, amma ga shi sun je domin su binciki zargin da sarakunan gargajiya su ka yi masu a jihar Zamfara.
You must log in to post a comment.