Rahotanni na cewa, Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, za ta gina jami’a mai suna ‘Jami’ar Muhammadu Buhari.
A’isha Buhari ta bayyana haka ne a garin Yola na jihar Adamawa, inda ta ce za ta hada gwiwa da kasashen Sudan da Qatar wajen gina jami’ar, amma ba ta bayyana inda za a kafa ta ba.Da ya ke na shi jawabi a wajen taron, Buba Marwa ya yi tsokaci a kan illar shaye-shayen, yayin da Sanata Silas Zwingina ya yi bayani a kan inganta ayyukan gwamnati, sannan Dakta Umar Bindir ya yi jawabi a kan matsanancin talauci da ake fama da shi a Nijeriya.