Home Labaru Kawallon Kafa: Yadda Ciniki Ya Kaya A Kan Dybala, Coutinho, Ozil, Da...

Kawallon Kafa: Yadda Ciniki Ya Kaya A Kan Dybala, Coutinho, Ozil, Da Eriksen

694
0
Ciniki Ya Kaya A Kan Dybala, Coutinho, Ozil, Da Eriksen
Ciniki Ya Kaya A Kan Dybala, Coutinho, Ozil, Da Eriksen

Ciniki ya fada tsakanin Tottenham da Juventus na sayen dan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala, mai shekara 25, a kan kudin da ya kai fan miliyan 62, kamar yadda labari ya bayyana.

Karanta Wannan: Magoya Buhari Sun Shirya Tarwatsa Zanga-Zangar Juyin Juya Hali

Yanzu Dybala zai fara tattauna yadda kwantiragin sa zai kasance da Tottenham kafin karshen wa’adin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta Ingila a ranar Alhamis.

Baya ga wannan kuma har yanzu Tottenham na sha’awar sayen dan wasan Barcelona na Brazil, Philippe Coutinho, mai shekara 27, yayin da wani rahoton ke cewa Arsenal ba ta taba nuna sha’awar ta a kan shi ba.

Ita kuwa kungiyar Amurka ta DC United rahotanni na cewa tana shirin tattaunawa da wakilan dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil, mai shekara 30, domin maye gurbin Wayne Rooney wanda zai tafi Derby, kamar yadda aka ruwaito.

Manchester United ta kara azama domin ganin ta sayi dan wasan tsakiya na Tottenham kuma dan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, kamar yadda jaridar Telegraph ta bayyana.

Eriksen ba ya daga cikin jerin ‘yan wasan da kociyan kungiyar ta Tottenham, Mauricio Pochettino, yake shirin amfani da su a nan gaba, kuma ya fitar da shi daga tsarin sa tun lokacin da dan wasan ya nuna cewa yana son sauya sheka.

United ta bullo da maganar neman sayen Eriksen ne sakamakon rashin tabbas na kasancewar dan wasanta na tsakiya, dan kasar Faransa Paul Pogba, mai shekara 26, na cigaba da kasancewa a kungiyar har zuwa karshen kasuwar yanzu.