Home Labaru Nasara: Dakarun Sojin Kasa Sun Kashe ‘Ƴan IPOB Da Jagoransu Ejike’ A...

Nasara: Dakarun Sojin Kasa Sun Kashe ‘Ƴan IPOB Da Jagoransu Ejike’ A Anambra

117
0

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe jagoran ƙungiyar IPOB da ESN masu fafutikar kafa ƙasar Biafra a Jihar Anambra da ke kudancin ƙasar.

Sanarwar da rundunar ta wallafa ta ce baya ga jagoran ƙungiyar mai suna Ejike da ta kashe yayin da suke tilasta wa mutane bin dokar da suka kafa ta zaman gida, ta kashe ƙarin wasu mutum uku.

Ta ce dakarunta sun fafata da ‘yan bindigar ne a kusa da wani gidan mai da ke yankin Ihiala.

Daga cikin makamai da ta ce ta ƙwace daga hannunsu akwai bindiga ƙirar gida biyu da babur ɗaya.

Sai dai rundunar ta ce sojojinta biyu sun rasa rayukansu sakamakon hatsari da motarsu ta yi yayin da ake kai dakaru wajen rikicin, sannan wasu biyu na kwance a asibiti.

Mutum biyun da suka rasu sun haɗa da jami’i da kuma kurtu.