Home Home Ziyara: Ta’aziyyar Hanifa Da Ahmad Bamba Ta Kai Aisha Buhari Kano

Ziyara: Ta’aziyyar Hanifa Da Ahmad Bamba Ta Kai Aisha Buhari Kano

38
0

Uwar gidan shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta kai ziyara Jihar Kano domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar kano mutuwar Hanifa Abubakar da kuma rasuwar fitaccen Malami, Dokta Ahmad Bamba.

A jawabin da ta yi wa manema labarai a Fadar Gwamnatin Kano, uwar gidan shugaban kasar ta ce ta kawo ziyara ne a domin ta yi ta’aziyya ga iyalan mamatan biyu.

A cewarta, “Na kawo ziyara nan Jihar Kano ne a karan kaina domin jajanta wa Gwamnan Jihar da matarsa, Sarkin Kano da kuma sauran mazauna jihar bisa rasuwar fitaccen malami, Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar.

“Muna addu’a kuma muna fatan za a yi mata adalci. A matsayina na uwa ina da ’ya’ya da jikoki da ke karatun Firamare yanzu haka, sun yarda da malaman su, mu ma iyaye mun amince da su.

Tun a farkon watan Janairu ne Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci kuma masanin Hadisi, Dokta Ahmad Ibrahim-Bamba rasuwa, inda dubun dubatar mutane ne suka halarci jana’izar a birnin Kano.