Home Home Rikicin Ukraine: Rasha Na Shirin Fara Atisayen Soja Da Belarus

Rikicin Ukraine: Rasha Na Shirin Fara Atisayen Soja Da Belarus

97
0

Rasha ta fara atisayen soja na kwana 10 tare da Belarus ana tsaka da fargabar girke dubban dakarunta a iyakar Ukraine.

Ana sa ran sojojin Rasha 30,000 ne za su shiga atisayen, sai dai mataimakiyar ministan tsaro Ganna Malyar ta ce babu alamun sojojin sun zo da niyyar tayar da husuma.

“Kan halin da ake ciki a bakin iyakarmu, muna iya ganin dandazon sojojin da suka mayar da hankali kan kafa kayan yaki, amma yanzu babu wannan, babu wata alamar barazana,” a cewar ministar.

Belarus babbar ƙawar Rasha ce kuma tana da iyaka mai tsayi da Ukraine ta kudanci.

Amurka ta bayyana atisayen  wanda ake ganin shi ne mafi girma da Rasha za ta yi a Belarus tun bayan yaƙin cacar baka – a matsayin “na tsokana”.