Home Labaru Nasara: Bazoum Ya Jinjinawa Sojojin Nijar

Nasara: Bazoum Ya Jinjinawa Sojojin Nijar

15
0
Shuganban Nijar

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bayyana cewar al’amuran tsaro sun sauya a Yankin Tillaberi inda dakarun gwamnati ke ci gaba da samun galaba akan ‘Yan ta’addan dake kai munanan hare hare.

Yayin da yake ganawa da dakarun gwamnati a ziyarar da ya kai jihar Tillaberi, shugaba Bazoum ya shaidawa sojojin cewar nasarar da suke samu ta sa ‘Yan ta’addar sake fasalin hare haren da suke kaiwa, yadda yanzu suka mayar da hankali akan fararen hula hare.

Shugaban kasar yace yanzu ‘Yan ta’addan basa iya kaiwa sojoji hari saboda sun san abinda yake jiran su, saboda haka sun mayar da hankali akan jama’ar da basa iya kare kan su.

Bazoum ya bayyana cewar ‘Yan ta’addan na kai hari akan manoman dake aiki a gonakin su a kauyukan da suke da yakinin cewar ba zasu gamu da sojoji ba.